12 Oktoba 2021 - 09:28
Tunisia: Majalisar Ministocin Sabuwar Gwamnatin Kasar Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki

Majalisar ministocin sabuwar gwamnatin kasar Tunisia karkashin firai minister Najlaa Budeen Ramadan ta yi rantsuwar kama aiki a yau Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : kasar Iran ya bayyana cewa firai ministan da kuma ministocinta duk sun yi rantsuwar kama aiki a gaban shugaban kasa Kais Sa’edd a yau Litinin.

A cikin jawabinda ta gabatar bayan rantsuwar kama aiki, Ramadan ta ce, muhimman al-amuran da gwamnatinta za ta sa a gaba su hada da farko dawo da yardar mutanen kasar ga gwamnati, da kuma tabbatarwa kasashen waje kan cewa mutanen kasar Tunisia su na iya tafiyar da al-amuransu ba tare da shigar kasashen waje ba.

A cikin sabuwar gwamnatin kasar ta Tunisia ministoci 25 dai, Usman Aljarandi ya ci gaba da rike kujerar ministan harkokin waje, a yayinda aka nada Taufiq Sharquddeen a matsayin sabon ministan cikin gida da kuma Ammad Mumish a matsayin ministan tsaro.

A ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata ne shugaba Kais Sa’eed ya rusa gwamnatin Hashim Mishishi sannan ya rusa majalisar dokin kasar. Banda haka ya ce zai gabatar da sauye-sauye a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

342/